Shugaba Muhammad Buhari ya umarci Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal kan ya warware Rikicin da ya barke a APC bayan kiran da tsohon gwamnan Lagos Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugaban jam'iyyar na kasa, John Oyegun da ya yi murabus, lamarin da ke neman wargaza jam'iyyar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a halin yanzu kai ya rabu a tsakanin membobin kwamitin zartaswa na jam'iyyar inda 'yan yankin Kudu maso Yamma suka marawa Tinubu baya wadanda ke ganin ana son kunyata tsohon Gwamnan ne.
Tun da farko dai, Mista Tinubu ya zargi John Odigie-Oyegun da yi wa "demokuradiyya zagon kasa" sakamakon rawar da ya taka a zaben fitar da gwani na jam'iyyar a jihar Ondo.
A wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Lahadi, jagoran na jam'iyyar APC ya ce Mista Oyegun ya karya ka'idojin demokuradiyya da aka shimfida jam'iyyar a kai.
Ya ce an kafa APC ne a kan turbar adalci da demokuradiyya, sai dai ya ce wadannan abubuwa na fuskantar barazana daga wadanda ba su da asali a jam'iyyar.
Sakamakon zaben na jihar Ondo, wanda Rotimi Akeredolu ya lashe, ya bar baya da kura, domin dan takarar da Tinubu ya ke goyon baya, Segun Abraham, ya yi watsi da shi.
Sanarwar ta Mista Tinubu ta ce wadanda suka kafa jam'iyyar sun fahimci cewa adalci ne zai sa ta karbu sannan jama'a su aminta da tsarin cigaban da aka kafa ta a kai. A cewarsa: "Idan jam'iyyar ba za ta yi adalci a kan kanta ba, to zai yi wuya ta samar tare da kafa gwamnati mai adalci a fadin kasar".
Title :
Buhari Ya Umarci Tambuwal Ya Sulhunta Tinibu Da Oyegun
Description : Shugaba Muhammad Buhari ya umarci Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal kan ya warware Rikicin da ya barke a APC bayan kiran da tsohon gwamnan Lago...
Rating :
5