A wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin Nijeriya, Shugaba Buhari ya amince a karbo basussuka daga cibiyoyin ba da lamuni na kasashen waje da nufin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa musamman wutar lantarki.
Da take karin haske game da batun, Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta ce za a karbo basussukan daga cibiyoyi masu saukin ruwa da suka hada da Bankin Duniya, Bankin Ci gaban Afrika, Bankin Exim na China, sai kuma Hukumar ba da lamuni ta Japan. Ta ce gwamnati za ta mika wannan bukata ga majalisar dokoki don amincewarsu.
Title :
Buhari Ya Amince A Karbo Basussuka Daga Waje
Description : A wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin Nijeriya, Shugaba Buhari ya amince a karbo basussuka daga cibiyoyin ba da lamuni na kasashen ...
Rating :
5