Gwamna Fayose na Jihar Ekiti yace Shugaba Buhari ne babbar matsalar Najeriya.
.
Gwamnan ya zargi Buhari da bata sunan ‘Yan Najeriya ta bayyanawa duniya cewa Mutanen Kasar barayi ko maciya amana ne. Fayose yace dole duk mai kishi ya tashi tsaye domin kare Najeriya daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari.
.
Fayose yace duk inda Shugaba Buhari ya sa kafa sai ya kira ‘yan Najeriya barayi kuma marasa gaskiya, hakan ya sa babu wanda zai shigo Kasar mutane marasa gaskiya da niyyar kasuwanci.
.
Gwamna Fayose yace Muhammadu Buhari ne ya sa masu jarin Kasashen waje suka tsere daga Kasar, da dabi’un sa da kuma kalamai.
.
Gwamnan na Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya koka da yadda tattalin arzikin Najeriya ya durkushe karkashin Shugaba Buhari.
.
Fayose ya zargi Shugaban Kasar da kin tuntubar masana harkar na tattali hatta a cikin Jam’iyyar sa ta APC. Gwamna Fayose yayi wannan jawabi ne a Garin Ado-Ekiti, inda ya tunawa Shugaba Buhari cewa a karshen mulkin sa.
.
‘Yan Najeriya za su duba aikin da yayi ne, ba abin da magabatan sa suka gagara yi ba.
.
Gwamnan ya kuma koka da tsananin yunwar da ake fama da ita a fadin Kasar nan, yace dole fa Buhari ya nema mana mafita.
.
Ayo Fayose yace Shugaba Buhari na mulkin kama-karya a Kasar, kuma ko kadan ba ya karbar shawarar wanda suke abokan gaba wajen siyasa, duk da cewa ita yunwa ba ruwan ta da Jam’iyya.
.
Fayose yace Gwamnatin Tarayya ta daina yi wa mutanen karya tana yaudarar su, Gwamnan yace wai don Gwamnati ta saki Naira Biliyan 350 zuwa ga ‘yan kwangila,
.
Wannan zai saukar da farashin shinkafa ne? Cewar Gwamnan Jihar Ekiti.
Aminiya Hausa
Title :
Buhari Ne Matsalar Kasar Najeriya - Ayo Fayose
Description : Gwamna Fayose na Jihar Ekiti yace Shugaba Buhari ne babbar matsalar Najeriya. . Gwamnan ya zargi Buhari da bata sunan ‘Yan Najeriya ta ba...
Rating :
5