Shugaban bankin raya kasashen Afirka na AfDB, Akinwumi Adesina, ya ce bakin zai tallafawa Nigeria da $10b domin shawo kan matsalar tattalin arzikinta.
Bankin dai zai bai wa Najeriya wadannan kudade ne a cikin shekaru uku a matsayin wani tallafi domin fitar da kasar daga matsin tattalin arzikin da ta shiga.
Mista Adesina ya ce AfDB zai fara bayar da $4.1bn a cikin shekarar 2016 da 2017.
Akinwumi ya kuma kara da cewa, bankin ya yi la'akari da irin zagon kasa da rashin isasshiyar wutar lantarki ke yi wa cigaban tattalin arzikin Najeriya adon haka zai zuba jarin wutar lantarki na megawatt 1,400 a bana.
Shugaban ya kuma ci gaba da cewa, bankin zai zuba jarin megawatt 1,387 a shekarar 2017 domin bunkasa bangaren wutar lantarkin kasar.
A lokacin da ya ke ganawa da kwamitin da ke kula da tattalin arzikin Najeriya, Mista Adesina ya ce: "Babu shakka kasar na cikin wani mawuyacin hali, amma kuma na yabawa gwamnatin Najeriya a kan jajircewarta na ganin cewar ta dauki kwararan matakai".
Mista Adesina ya jadadda cewa yana da muhimmanci sosai kasar ta rage dogaro da man fetur ta mai da hankali kan noma da ma'adinani da kuma bunkasa bagaren masana'antu .
Ya kuma kara da cewa bankin zai tallafawa bankin cigaba na Najeriya da $500m domin tallafawa bangaren tattalin arziki da ke samar da kayayyaki da kuma wajen cigaban mata da matasa a kasar.
Bankin zai kuma bai wa bankin masana'antu na Najeriyar $100m domin ya tallafawa kananan masana'antu da rance.
Shugaban na AfDB ya jaddada cewa tattalin arzikin Najeriya na cikin wani mummunan yanayi, amma kuma ya kara da cewa "ba zai ruguje ba".
Ya ce idan mutane suna ikirarin cewa kasar na fama da matsalar matsanancin bashi, amma a gaskiya kasar ba ta fama da bashi a cewarsa.
A ranar Litinin ne dai shugaban AfDB din ya fara ziyarar aiki ta kwana biyu, wadda ita ce ziyararsa ta farko a kasar, tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban bankin a bara.
Source BBC HAUSA
Title :
Bankin Afirka Zai Tallafa Wa Najeriya Da $10b
Description : Shugaban bankin raya kasashen Afirka na AfDB, Akinwumi Adesina, ya ce bakin zai tallafawa Nigeria da $10b domin shawo kan matsalar tattalin ...
Rating :
5