Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce bai ga dalilin da zai sa ace ya yi yar shugaban kasa Zahra Buhari tsufa da aure ba. Duk da dai wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa jaridar Pointblanknews.com cewa, janar Muhammadu Buhari ya yi masa gargadi mai tsauri akan ya nisance Zahra. Sakamakon yunkurin da gwamnan ke yi na ganin ya sure ta a matsayin amaryar sa.
“Me ye matsala don na auri Zahra? Shekarun ta 21 shekaruna 49. Shin Ni ne mutum na farko da zan auri budurwa? Ko ba ku da labarin mutanen da su ke auren 'yar shekara 12?" A cewar Gwamna Yari yayin zantawa da Pointblanknews.com ta bakin hadiminsa ta fuskar yada labarai Mallam Ibrahim Dosara.
Madogara: Jaridar The Punch.
Title :
Ban Yi Tsufa Da Auren Zahra Buhari Ba - Gwamnan Zamfara.
Description : Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce bai ga dalilin da zai sa ace ya yi yar shugaban kasa Zahra Buhari tsufa da aure ba. Duk da dai w...
Rating :
5