Kungiyar Malaman jami’o’i ASUU ta bayyana wa ‘yan Najeriya cewa, ba ta da wani shirin fara yajin aiki da zai fara daga 2 ga watan Oktoba kamar yadda wakilin kungiyar daga Jami’ar Abuja, Ben Ugheoke, ya bayyana wa manema labarai.
A jiya Talata ne kamfanin dillancin labarai NAN ya bayyana wani rahoto da ke cewa kungiyar za ta fara yajin aiki daga watan Oktoba, bayan tattaunawar da Ugheoke ya yi da manema labarai ya ce babu batun yajin aikin kamar yadda ake ta yadawa.
Title :
Bamu Da Niyar Shiga Yajin Aiki - ASUU
Description : Kungiyar Malaman jami’o’i ASUU ta bayyana wa ‘yan Najeriya cewa, ba ta da wani shirin fara yajin aiki da zai fara daga 2 ga watan Oktoba k...
Rating :
5