Kwamitin Masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Unguwar Sarki cikin
garin Kaduna, karkashin jagorancin shugaban kwamitin Sheik Hamisu Ya'u,
ya bada sanarwar dakatar da babban limamin masallacin Sheik Abdulhameed
Balele Wali daga limanci har abinda hali ya yi, tare da maye gurbin sa
da Na'ibinsa, Malam Ibrahim Alaramma.
Kwamitin Masallacin ya dauki matakin dakatar da limamin ne biyo bayan
wata hatsaniya da aka samu a masallacin a safiyar ranar Sallah lokacin
gudanar da sallar idi a masallacin na Sultan Bello a ranar Litinin da ta
gabata.
Hayaniyar dai ta samo asali ne sakamakon tashi da hadari
da aka yi a ranar, dalilin da ya sanya aka bar filin idi aka koma cikin
masallaci, ana cikin masallacin ne ruwan sama ya fara sauka, shi kuma
Liman bai rigaya ya iso ba, sakamakon korafi da damuwar jama'a ya sanya
aka bukaci Dakta Ahmad Gumi da ya bada sallah, yana cikin gabatar da
sallar ne sai Liman Malam Balele Wali ya karaso, bayan an kammala sallah
ne sai Dakta Gumi ya tashi domin gabatar da huduba, shi kuma Malam
Balele Wali sai ya yunkura ya rike Daktan tare da kokarin hana shi
karanta hudubar, lamarin da ya haifar da hatsaniya har wasu matasa suka
kwashi Liman din suka yi waje da shi.
Da yake karin haske a gaban
manema labarai shugaban kwamitin Sheik Hamiu Ya'u ya ce daukar matakin
dakatar da limamin ya zama wajibi domin gudanar da kyakkyawan nazari
tare da daukar matakin da ya dace a nan gaba.
source Rariya
Title :
An Dakatar Da Limamin Masallacin Juma'a Na Sultan Bello Dake Jihar Kaduna
Description : Kwamitin Masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Unguwar Sarki cikin garin Kaduna, karkashin jagorancin shugaban kwamitin Sheik Hamisu...
Rating :
5