A karon farko an haifi wani jariri da aka hada kwayar halittarsa daga mutane uku cikin mahaifa guda.
Mujallar Kimiya da ake kira ‘Scientist Magazine’ ta ce an haifi jaririn ne watanni biyar da suka gabata a kasar Mexico kuma iyayensa ‘yan kasar Jordan ne, sannan yana cikin koshin lafiya.
Rahotanni sun ce mahaifiyar yaron na dauke da wata cutar da tayi sanadiyar mutuwar ‘ya’yan ta guda biyu, kana tayi bari sau hudu.
Ganin wannan matsala ya sa matar ta nemi taimakon wani likita a New York mai suna John Zhang dan samun jaririn da ba zai samu cutar da take dauke da shi ba.
Likitan ya dauki kwan matar da mijin ta, inda aka hada dana wani wanda ya bada gudumawa wajen samun ‘dan a kasar Mexico ganin Amurka ta haramta yin haka a cikin kasar ta.
Ana saran likitan da abokan aikin sa suyi bayani kan hanyoyin da suka bi wajen hada kwayoyin halittar ga Hukumar kula da haihuwa ta Amurka a watan gobe.
Rfi hausa
Title :
Al'ajabi: An haifi Jariri Mai Iyaye 3 A Kasar Mexico
Description : A karon farko an haifi wani jariri da aka hada kwayar halittarsa daga mutane uku cikin mahaifa guda. Mujallar Kimiya da ake kira ‘Scientist...
Rating :
5