ƊANƊANO.
"Ta yaya za'ayi na rayu babu soyayyar Yaya
Khalid a tare dani?? Idan kuma dole sai na rayu a
duniyar da babu soyayya, shin wace hanya zan bi
dan na kawar da soyayyar Yaya Khalid daga
Zuciyata??" waɗannan tagwayen tambayoyi, sune
waɗanda kusan kullum a wancan lokacin sai na
yiwa kaina. Amma sam ban taɓa samun amsar
ko ɗaya daga cikinsu ba...
Akan soyayyar Yaya Khalid wanda aka nesantani
dashi, na roƙi Allah ya ɗauki raina amma har
yanzu ciwon kai bayi ba bare in sa ran mutuwa,
har ta kaini ga ina yin nafilolin dare ina roƙon
Allah ya kasheni amma rayuwata bata bar
wannan duniyar ba. Hakan yasa daga ƙarshe na
haƙura da samun Yaya Khalid na rungumi
ƙaddarata.
.
Oops! Kar nayi nisa da baku labarina ba tare da
kunsan sunana ba!
Sunana ZAREENAH ƴ'ar shekaru 19, haifaffiyar
garin Kaduna, ina zaune a gidan wan mahaifina
tun lokacin da nake da shekaru 7 a Duniya.
Hakan ya samo asaline daga rashin iyayena da
nayi, kusan lokaci ɗaya na rasasu.
Babana ya rasu ta hanyar haɗarin mota, sanadin
kamuwar hawanjini kenan da Mamata tayi da har
itama ta bishi.
Alhaji Abdullahi wato yayan Baban nawa, shine ya
raineni tare da taimakon Hajiya Sa'adatu wacce
ta ɗaukeni tamkar ƴ'ar da ta haifa da cikinta.
Na samu gata na ƙin ƙari, dan wasu lokutan har
nikan manta da cewa iyayena basa Duniya.
A nan na haɗu da ƴ'aƴ'ansu Yaya Khalid da kuma
Yaya Mus'ab, muna rayuwarmu cikin farin ciki da
walwala...
Anty Habiba wato autar su Babana ita kaɗaice
cikas ɗina a gidan, bansan me nayi mata ba da
har ta tsaneni haka. Ko giftawa nazo yi a
gabanta, inda su Umma basa kusa to na shiga
uku da ita...
Yaya Khalid shine yake ɗaukana muje yawo cikin
gari, ya kaini gidan zoo, ya kaini Shoprite muyi
siyayya, a gida kuma kullum muna tare indai
ranar baya zuwa makaranta, haka ya taimaka
sosai waje ƙarin shaƙuwata dashi.
Ina Primary 5, Baba yace zai tura Yayana
England ya ƙaro karatu akan Kasuwanci, ba
ƙaramin ɓacin rai da baƙin ciki naji ba. Amma haka
na jure ya tafi...
Yaya Mus'ab shine ya cigaba da kwatanta yi
mani yadda Yaya Khalid yake mun, amma sam
bana nishaɗantuwa saboda bai san halayena
kamar yadda Yayana ya sani ba...
.
.
*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*
Kan teburin cin abinci (DINNING TABLE) suke,
kowanne ya ja kujerarsa ya zauna.
A saman teburin, manyan FoodFlasks ne an
jerasu reras! Da zan buɗe muku kuga irin nau'in
abincin dake ciki, da a buɗe zaku bar bakunanku
cikin mamakin ko za'a iya samun kukun da zai
iya dafa irin wannan abincin a Nigeria??
Wannan aikin Amina kenan, ƴ'ar aikin gidan wacce
ta kai a ƙalla shekaru 8 a gidan, yanzu tana da
shekaru 22 a Duniya, har ta zama ƴ'ar gida kuma
aminiyar Zareenah, kusan ince ita kaɗai take
bawa sirrinta. Tana da ɗakinta a gidan kuma ba
abinda zata nema face ta samu. Kafin ma ta fara
aiki a gidan, saida Hajiya Sa'adatu wacce ta
ɗaukota daga ƙauye ta kaita makarantar koyon
girki sannan ta shigo gidan.
Alhaji Abdullahi ne zaune akan kujerar gaban
teburin, a gefen damansa Zareenah ce riƙe da
Spoon. Allah-Allah take Baba ya gama Addu'a ta
hau cin abinci.
A gefen hagu Hajiya Sa'adatu ce ta hakimci,
gefen Zareenah kuma Yaya Mus'ab ne sanye da
rigar Dolce & Gabbana.
Gefen Hajiya kuwa, Anty Habiba ce tana fuskantar
Zahreenah tana haranta cikin taku...
"Bisimillah." haka Daddy ya furta bayan sun shafa
Addu'a, nanfa aka fara gumurzu da cokula.
Ba'ayi nisa da fara cin abincin ba, sai Dad ya
ɗago kai yana kallonta yana murmushi yace
"Auta albishirinki." kanta ta ɗago ta murƙushe
naman kaza dake bakinta, bata samu cewa komi
ba saida ta haɗiye sannan tace "farin goro sal!
Daddy." Mus'ab yana murmushi yace "kedai ci a
hankali." Dad yace "yanzu haka da muke magana,
Yayanki yana kan hanyar dawowa gida."
"DA GASKE???" ta faɗi haka tana ɗaga muryarta
cike da murna, ganin haka yasa Anty Habiba ta ja
tsaki tace "to meye kuma na tsalle a ciki??" Mom
ta ajiye cokalin dake hannunta tace "A'a barta
tayi, banga laifinta ba." labarin da Daddy ya
bayar yasa Zareenah jin wani mugun daɗi.
Musamman idan ta tuna yau shekaru biyar kenan
da ya tafi England, duk da chatting da kuma turo
mata da hotunansa da yakeyi hakan baya gamsar
da ita sosai, burinta shine ta ganshi tsaye a
gabanta.
Bata gama cin abincin ba, haka ta miƙe ta nufi
hawan sama inda ɗakinta yake "ina kuma zakije
ba'a gama cin abinci ba?" Mom ta aika mata da
tambayar da yasa ta waigo tace "Mom, wayata
zan ɗauko muyi chatting in ɗebe masa kewa kafin
ya sauko daga jirgi." Mus'ab ya yamutse baki
yace "kaji wani sabon salo! Wai ɗebe kewa,
c'mon dawo ki zauna, ko bakya so ya dawo ya
ganki kin canja ne??" jin haka yasa ta dawo ta
zauna.
Zamanta keda wuya, sai idanuwanta sukayi tozali
da Anty Habiba ta haɗe mata fuska saida
gabanta ya faɗi.
Title :
Zareenah Part 1
Description : ƊANƊANO. "Ta yaya za'ayi na rayu babu soyayyar Yaya Khalid a tare dani?? Idan kuma dole sai na rayu a duniyar da babu soyayya,...
Rating :
5