A wani mataki na yin raddi ga 'yan Kudu da ke matsin lamba kan sake fasalin Nijeriya, daya daga cikin membobin majalisar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa za a iya raba Nijeriya idan har wasu na ganin Turawan Mulki sun yi kuskure wajen hade Kudu da Arewa a matsayin kasa daya.
Farfesa Abdullahi ya yi wannan ikirarin ne a wurin bikin kaddamar da wani littafi game da tarihin Umar Turakin Bauchi inda ya nuna cewa Arewa ba ta tsoron a raba Nijeriya yana mai cewa manyan kasashe kamar su Indiya su rabe a inda aka fitar kasashen Pakistan da Bangaladash.
Ana dai ci gaba da kiraye kirayen sake fasalin Nijeriya, matakin da Shugaba Buhari ya nuna rashin amincewa da yin hakan. Daga cikin masu irin wannan ra'ayi na neman sake tsarin Nijeriya, har da tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Title :
Za A iya Raba Nijeriya Kowa Ya Kama Gabansa- Farfesa Abdullahi
Description : A wani mataki na yin raddi ga 'yan Kudu da ke matsin lamba kan sake fasalin Nijeriya, daya daga cikin membobin majalisar dattawan Arewa,...
Rating :
5