Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta haramta gudanar da bikin aurar da Zawarawa da kungiyar nan da ke biyayya ga tsohon Gwamnan jihar ta Kwankwasiyya ta shirya yi.
Da yake karin haske kan haramcin, Jami'in Hulda da Jama'a na rundunar, Magaji Majiya ya nuna cewa bikin ya ci karo da wani shirin gwamnatin jihar na tallafawa matasa wanda aka tsara yi a jibi Asabar.
Ya ci gaba da cewa rundunar ta samu bayanan sirri kan cewa wasu bata GARI na shirin rabewa da bukukuwan wajen tayar da hankalin jama'a inda ya nuna cewa Kwamishinan 'yan sandan jihar zai zauna da bangarorin biyu don ganin an samu maslaha.
Title :
Yan Sanda Sun Haramta Shirin Auren Zawarawa Na Kwankwasiyya
Description : Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta haramta gudanar da bikin aurar da Zawarawa da kungiyar nan da ke biyayya ga tsohon Gwamnan jihar ta ...
Rating :
5