A Najeriya, rahotannin da ke fitowa daga jihar Ogun ke cewa 'yan sanda sun saki matashin nan da ya sanya wa karensa suna Buhari.
An sako Joe Chinakwe ne bayan shiga tsakani da kungiyar kabilu wadanda ba 'yan asalin jihar ba ne suka yi da rundunar ta 'yan sanda.
An dai ce mutumin ya rubuta sunan 'Buhari' a jikin karen ne, abin da ke nufin sunan da ya sanya masa ke nan.
Bayanai sun nuna cewa Joe yana da makwabci mai suna Buhari wanda kuma ba sa ga maciji da juna.Kuma makwabcin nasa ne ya kai karar sa ga 'yan sandan jihar, a inda 'yan sandan suka cafke shi.
Bbchausa
Title :
Yan Sanda Sun Sake Mutumin Da Ya Sawa Sunan Karensa Buhari
Description : A Najeriya, rahotannin da ke fitowa daga jihar Ogun ke cewa 'yan sanda sun saki matashin nan da ya sanya wa karensa suna Buhari. An sak...
Rating :
5