Rundunar 'yan sanda ta jihar Ogun na tsare da wani dan kasuwa dan kabilar Igbo mai suna Joe Chinakwe sakamakon zargin da ake masa na sanyawa karen sa suna Buhari.
Makwafcin shagon wannan Igbo wanda kuma Bahaushe ne dan Arewa shi ya kai kara ofishin' yan sanda na Sango dake cikin kasuwar da suke, wacce akasarin ta 'yan Arewa ne ke harkokin su na cinikayya a ciki, inda kuma ya yi zargin makwafcin sa ya sa wa karensa sunan Buhari.
Bayan an kama wannan dan kasuwa' yan sanda sun gano gaskiyar zargin da ake yi masa, duk By kuwa da cewa ya bai wa abokansa Igbo damar su yanka karen su cinye gudun kar a fallasa shi.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan uwanta Chinakwe sun nemi belin dan uwa su amma' yan sanda sun hana saboda fargabar abin da zai biyo baya idan an sake shi ya shiga gari, domin kuwa an ce abin da ya faru ya yi matukar tunzura Hausawa mazauna garin da abokan kasuwancin sa.
Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da tsare wannan Igbo da ya ce za a gurfanar a gaban kotu, don a yanke masa hukuncin da ya dace da laifin da ya aikata.
Title :
Yan Sanda Sun Kama Wani Dan Kasuwa Saboda Ya Sawa Karensa Suna Buhari
Description : Rundunar 'yan sanda ta jihar Ogun na tsare da wani dan kasuwa dan kabilar Igbo mai suna Joe Chinakwe sakamakon zargin da ake masa na san...
Rating :
5