An kama shahararren mawaki Chris Brown da zargin kai wa wata hari da makami bayan matar ta shaida wa 'yan sanda ya yi mata barazana da bindiga.
Beauty Queen Baylee Curran ta shaidawa jaridar LA Times da ke Amurka cewa Mista Brown ya nuna mata bindigar shi a fuskar ta bayan ta bayyana sha'awarta ga sarkar abokinsa.
A ranar Talata ne dai Mista Brown ya fito daga gidansa bayan wata sa'insa da ya yi da 'yan sanda.
Kamfanin dillacin labarai na AP ya rawaito cewar an sallami Mista Brown a kan belin $250,000
An sha samun mawakin da laifukan tayar da hankali, ciki har da cin zarafi da ya yi wa budurwar sa Rihanna a shekarar 2009.
Bbchausa
Title :
Yan Sanda Sun Kama Chris Brown
Description : An kama shahararren mawaki Chris Brown da zargin kai wa wata hari da makami bayan matar ta shaida wa 'yan sanda ya yi mata barazana da b...
Rating :
5