Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wasu matasa uku dake satar mutane wadanda kuma ake zargi da sace dan majalisar wakilai daga jihar Katsina Hon Sani Bello Mashi.
Matasan sun hada da madugun barayin wato Haruna Adamu mai shekaru 25 da haihuwa, sai Shu’aibu Adamu mai shekaru 18, da kuma Abubakar Sa’idu mai shekaru 30.
An sami kudi Naira dubu dari biyu da hamsin a kauyen binne a kauyen daya daga cikin barayin da aka kama su a karamar hukumar Dan’dume dake jihar katsina. An kuma sami wayar salular da barayin suka yi amfani da ita wajan neman kudin fansa.
Sabon mukaddashin ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya dora aniyar yaki da miyagun iri. Hakan yasa damke wadanda suka sace
jami’in diflomasiyyar kasar Saliyo Alfred Nelson, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Wadanda suka zanta da tun farko da masu garkuwa da mutanen domin sako dan majalisa Sani Mashi, sun tabbatar wadanda ake zargin Fulani ne, kuma hakan ne yasa sabuwar kungiyar Fulani ta taso da kamfe din yaki da miyagun iri a cikin matasan Fulani.
Shuganam kungiyar ta Abuja Malam Abubakar Suleman ya bayyana cewa a shirye suke domin ba jami’an tsaro hadin kai dari bisa dari domin tabbatar tankade duk wani mugun iri a tsakanin kabilar, ya kara da cewa kamar yadda wannan sabuwar gwamnati ta kawo canji, suma baza’a barsu a bay aba wajan tabbatar da samar da canji a tsakanin matasan Fulani.
Title :
Yan Sanda Sun Cafke Matasa Uku Masu Satar Mutane A Jihar Katsina
Description : Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wasu matasa uku dake satar mutane wadanda kuma ake zargi da sace dan majalisar wakilai daga jihar Kat...
Rating :
5