|
Falalu Dorayi Acikin fim Din UMAR SANDA |
Shahararren Mai bada Umarni kuma Jarumi haka za lika mai shirya fina-finai, wanda kuma shike da kamfanin DORAYI ENTERTAINMENT dake motsawa a Masana'antar fina-finan Hausa. Falalu A Dorayi ya bai yana mana matsayinsa a fim din UMAR SANDA, Jarumin dai ya fito ne a matsayi wani Dan sanda mara Imani wanda yake zalintar Al'umma a cikin shirin fim din, wanda bashi da tausayi ko kadan inda yake gallaza wa mutane.
Kafin daukar fim din dai Jarumin yabar gemu mai tsawo, amman yayin daukar shirin sai da akasa Jarumin ya aske dan yayi dai dai da role din da zai hau a cikin shirin, sanin kowane 'Yan Sanda ko duk wani Jami'in tsaro yana aske Kanshi tsaf ko yayi aski amman zai bar dan gashi kadan, ko dayake wannan anfi samun shi ga jami'an 'Yan Sanda inda zaka ga sunyi aski sun dan bar gashin baki. Falalu dai yayi irin wannan aski dan ya fito kaman yadda Jami'an tsoro suke dan kuma masu kallo suga da gaske ne.
Bayan gama wannan fim din dai Jarumin ya tattaro inashi inashi ya dawo gaban iyalinsa ne, da shigan sa gidan 'yar sa ta rugo ta mai oyoyo bayan ya dauketa ne sai ta kula da gemun da take wasa dashi babu an aske taga mahaifin nata ya dai chanja ba yadda ta saba ganinshi ba, abinka da yaro akan abinda ya saba gani sai yaga ya banbanta, annan ne fa ta zame ta koma gun mahaifiyarta, sannan mai dakin nasa tasanar dashi fa bata gane ka bane, inda ya gwada kara daukar ta taki, ta nuna sam ba mahaifin nata data sani bane.
A cewar Jarumin gaskiya abin ya matukar bashi mamaki dan kwana biyu da dawowarsa amman bata amince dashi kaman yadda suka saba wasa ba, yana ganin zai yi wuya ya kara yin irin haka wanda zai sa yaran sa suga kaman bashi bane, indai ba wata hikimar za'ayi ba kamar yadda sukeyi a cikin fina-finai ta chanjawa mutum wata sura ko kaman ni ba.
Falalu Abubakar Dorayi dai ya bada umarni a fina-finai da dama wanda har ya samu lashe kanbu da dama a masana'antar ta haryar bada Umarni, a yanzu kuwa yana daga cikin Jaruman dake Nishadantar da Jama'a a cikin fina-finai musamman a barayin barkwanci (Comedy). Jarumin dai ya fito a fina-finai da dama ga kadan daga cikin su NAS, GWASKA, BABBAN YARINYA, BABBAN YARO, NA HAUWA, TEBURIN MESHAYI, Da dai sauransu. Fim din UMAR SANDA Mai Shadda Ya Shirya, Kamal.S Alkali ya bada Umarni.
Kalli Trailer Fim Din UMAR SANDA Akasa
Title :
Video: Fim Din UMAR SANDA Yasa 'Yata Ta Gujeni - Falalu Dorayi
Description : Falalu Dorayi Acikin fim Din UMAR SANDA Shahararren Mai bada Umarni kuma Jarumi haka za lika mai shirya fina-finai, wanda kuma s...
Rating :
5