Daga Leaders Hausa
Sakamakon hadarurrukan motar da suka zama ruwan dare a kan titin gwamnatin tarayya a yankunan Kunya-Kanya Babba, Babura wadda ya yi sanadiyyar rasa rayukan daruruwan mutane, al’ummar yankunan sun nemi gwamnati ta kawo musu dauki domin ceto rayuwar al’umma a yankin.
Wannan kira na kunshe cikin wata takarda da suka mika kwafinta ga Sanatan da ke wakiltar yankinsu na Jigawa ta Tsakiya, ministan ayyuka na gwamnatin tarayya domin share musu hawaye.
Takardar wadda ta ke dauke da sahannun wata kungiya mai radin kishin yankin Babura (BAPM), da kuma wata ta matasa masu kokarin ciyar da yankin gaba (BYDI), ta bayyana wannan titi da sunan “Ajalin al’umma.”
Haka kuma sun bayyana damuwarsu matuka bisa yadda gwamnatocin baya suka nuna halin ko-inikula kan titin duk da cewar kullum yana cigaba da sanadiyyar rasa rayukan mutane da dukiyoyi masu tarin yawa.
Takardar ta ci gaba da cewa, shi dai wannan titi an gina shi tun kimanin shekaru 43 da suka gabata kuma tun tsawon wannan lokaci gwamnatin tarayya ba ta taba yiwa titin wani kwakkwaran gyara ba har zuwa wannan lokaci.
Haka kuma takardar ta bayyana cewa bayan asarar rayuka da ta dukiyoyi da ake yi, lalacewar titin ta kuma yi sandiyyar durkushewar harkokin kasuwanci a yankin baki daya.
Title :
Titin Gwamnatin Tarayya Ya Zama Ajalin Al’umma A Jigawa’
Description : Daga Leaders Hausa Sakamakon hadarurrukan motar da suka zama ruwan dare a kan titin gwamnatin tarayya a yankunan Kunya-Kanya Babba, Babura ...
Rating :
5