Sakamakon bayanan sirri da dakarun sojojin Nijeriya suka samu daga wurin 'yan kasa nagari, dakarun sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne masu suna a Dayibu Abdullahi da Nasiru Adamu, a kauyen Badiko dake kusa sa da titin Gumau a karamar hukuma Toro, a jihar Bauchi..
Haka kuma sojojin sun gano kudi kimanin naira dubu 439 a hannunsu. Wanda kuma bincike ya nuna cewa kudin wani kaso ne na kudin da aka yi fansar wani da suka yi garkuwa da shi.
A wani labari makamancin haka ma, an kama wani mai suna Jibrin Dakam a yankin Magama dake karamar hukuamar ta Toro, inda shi ma ake zargin yana daga cikin masu garkuwa da mutane ne.
Source Rariya
Title :
Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Bauchi
Description : Sakamakon bayanan sirri da dakarun sojojin Nijeriya suka samu daga wurin 'yan kasa nagari, dakarun sun yi nasarar kama wasu mutane biyu...
Rating :
5