Daga Bashir Ladan Yuguda
Tunda nake a rayuwata ban taba jin wani yace kwana uku baici abinci a gidan sa ba Sai kwanan nan kowa yanzu kansa ya sani mutane masu karfi sun koma bara saboda ba aikinyi kuma ba kudi a hannunsu sun fita Neman aikin babu to ina zasu saka kansu ? Shuwagabanni mu Wai Har Suna iya bacci a hakan Suna iya cin abinci Suna iya dariya waiyazu billah malaman mu sunyi shiru sun zuba ido ana ta tabka kuskure amma baza'a fada musu ba saboda gidanku ba'a kwana da yunwa kuma Kuna samun kyauta daga hannunsu to Ku sani idan Har baza Ku fada musu ba mu zamu fada musu cewa su sani akwai mutuwa akwai kuma tashin alkiyama sannan akwai hisabi to me kuka tanadar don Ku fada ma ubangiji yanda kuka gudanar da mulkin Ku ga Al ummah? Shin Baku tunanin wadannan abubuwan zasu faru kuma ubangiji ya maka tambaya mutum nawa suka kwana da yunwa lokacin mulkin Ka mutum nawa suka mutu basu da kudin magani shin Ka manta da tambayoyin kabari ne ko Ka manta kullum kana tafiya tare da malaiku ne to shuwagabanni mu kuji tsoron Allah Ku sani talakawa Suna shan bakin wahala Kuyi tunani akan duk abunda na fada shine ainihin soyayya ta a gareku.
Bashir Ladan yuguda
24 - 08 - 2016
08033609598
Title :
Shuwagabanni Mu A Wannan Zamani Da Yawa Yan Wuta Ne
Description : Daga Bashir Ladan Yuguda Tunda nake a rayuwata ban taba jin wani yace kwana uku baici abinci a gidan sa ba Sai kwanan nan kowa yanzu kansa ...
Rating :
5