Hukumomin Saudiyya ta saki mahajjatan Nijeriya daga jihar Kwara da aka kama a masarautar bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa ( NAHCOM) ce ta sanar da haka inda ta nuna cewa bincike ya tabbatar da cewa an kama mutanen biyu bisa kuskure bayan da aka gudanar da cikakken bincike.
A cewar hukumar Alhazan, a halin yanzu mahajjatan sun ci gaba da gudunar da ayyukan hajji su kamar sauran takwarorinsu daga jihar Kwara.
Source Rariya
Title :
Saudiyya Ta Saki Mahajjatan Da Ake Zargi Da Fataucin Kwayoyi
Description : Hukumomin Saudiyya ta saki mahajjatan Nijeriya daga jihar Kwara da aka kama a masarautar bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi. Hukumar Jin ...
Rating :
5