Daga Jaridar Rariya
A jiya Litinin ne Allah ya yi wa Sarkin garin Ankpa, Yakubu Ahmodu, rasuwa bayan ya yi shekaru 73 a duniya sakamakon gajeruwar rashin lafiya da ya yi.
Wata majiya daga fadar masarautar ta bayyana mana cewa marigayi Sarkin, a ranar Lahadin da ta gabata ya halarci taro kan harkokin Musulunci da aka gudanar a garin Benin kafin ya bar duniya a washegari.
Marigayin ya hau sarauta ne a ranar 7 ga Agusta, 1993. Ya rasu ya bar mata, yara da jikoki da dama.
Title :
Sarkin Garin Ankpa Dake Jihar Kogi Ya Rasu
Description : Daga Jaridar Rariya A jiya Litinin ne Allah ya yi wa Sarkin garin Ankpa, Yakubu Ahmodu, rasuwa bayan ya yi shekaru 73 a duniya sakamakon g...
Rating :
5