Via Auwal G Danbarno
Da za'a yi hakuri a rufe bodar nan, tsawon shekaru goma ko fiye da Arziki ya wadata. Dan rufe bodar nan da aka yi ya sanya da yawan mutane bana sun yanki daji sun fara noma.
Wasu ma kamar ni ba mu San cewa muna da Gonaki da Muka gada a wajen kakanni ba. Haba jama'a duk mutanen kauye sun zo birni Sun tare ba tare da wata ingantacciyar sanaa ba. Sai ka ga garjejen kato yana tallar raken da bai fi na Nera dari biyu ba duk jarin, ko yankan farce dss. Duk sun baro gonakansu ciyawa ta cika su. Yanzu da suka ga abin ya ci uwar mai shayi kowa ya Koma gida. Tun kaka ba ta shigo ba har abinci ya fara saukowa duk da cewa wannan shekarar ba wani tallafi daga gwamnati. Tabbas shekara mai zuwa muna sanya rai shinkafa za ta dawo dari biyu kwano daya duk kyan ta.
Title :
Sai Yanzu Na Gane Dalilin Rufe Boda
Description : Via Auwal G Danbarno Da za'a yi hakuri a rufe bodar nan, tsawon shekaru goma ko fiye da Arziki ya wadata. Dan rufe bodar nan da aka yi ...
Rating :
5