Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta rufe gidan Tsohon Gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso bayan aurar da Zawarawa 100 da gidauniyarsa ta Kwankwasiyya ta yi a asirce.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka ci gajiyar auren sun yi dafifi a gidan wanda ke titin Nasarawa GRA don karbar kyaututtukan da aka yi masu alkawari.
Idan ba a manta ba, rundunar 'yan sandan jihar ta haramta gudanar da bikin Auren tun a makon da ya gabata bayan rahotannin cewa wasu na son amfani da wannan dama wajen tayar d rikici.
Title :
Rundunar 'Yan Sanda Ta Rufe Gidan Kwankwaso
Description : Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta rufe gidan Tsohon Gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso bayan aurar da Zawarawa 100 da gidauniyars...
Rating :
5