A yau ne jami'an tsaro suka cafke wani Sojan gona mai amfani da sunan fitaccen mawakin finafinan Hausan nan Mura M. Inuwa a garin Kano.
Wannan matashi mai suna Umar, ya kasance yana amfani da sunan Nura M Inuwa a shafukan sada zumunta na yanar gizo, irinsu Facebook, whtsapp, da sauransu.
Sannan yana yin shiga irin ta Nura M Inuwa komai da komai, kasancewar sun so su yi kama da juna, wanda hakan ya ba shi damar damfarar mutane yana karbar masu kudi akan shine M Inuwa.
Wata majiya ta ce har kudi yake karba ana gayyatar shi wasa a gidajen biki da na dirama, inda yake hawa wakokin Nuran .
Rahotanni masu bugun juna sun tabbatar da cewa dubun wannan matashin ta cika, domin a jiya 'Yan sanda a garin Kano suka yi awon gaba da shi suka kai shi ofishinsu suka kulle, daga bisani yau aka mika shi gaban alkali a kotun 'Yan Alluna dake unguwar Fagge. Inda alkali mai shari'ar ya bada umarnin a kai shi gidan yari sai nan da sati biyu za'a nemi 'yan uwansa sannan a ci gaba da shari'ar.
Title :
Photos: Yan Sanda Sun Kama Wanda Yake Damfara Sunan Nura M Inuwa
Description : A yau ne jami'an tsaro suka cafke wani Sojan gona mai amfani da sunan fitaccen mawakin finafinan Hausan nan Mura M. Inuwa a garin Kano. ...
Rating :
5