Sojojin Najeriya sun burge mutane da yawa wajen gina makaranta ta yara a sansanin gudun hijira(IDP) wanda a ke garin Bama, Jihar Borno. Makarantar wucin gadin anyi ta ne da runfunan sojoji wanda bataliya ta 21, kashi na 7 na sojojin Najeriya suka hada.
A cewar mai magana da bakin sojojin wato Colonel Sani Kukasheka Usman yace “Makarantar ta hada da runfunan sojojin guda 6 wanda sojojin da basu ke aiki ba ranar suke koyarwa Haka kuma, wasu yan gudun hijirar wadanda a da malami ne suma suna koyarwa a makarantar”.
Wannan shirin ya ja hankalin majalisar dinkin duniya dake kula da ilimin yara (UNICEF) wanda ta taimakama bataliyar da Karin rumfuna 2 da jikkunan makaranta ga yaran. Ita kuma hukumar dake kula da ilimin zamani na Jihar Borno ta aiko shugaban makaranta don taimakawa wajen gudanar da makarantar.
Mr Tobby Lanzer wanda shine babban mataimakin sakatare ne a majalisar dinkin duniya kuma mai daidaita jin dadin al’umma yankin Sahel ya yabama sojojin Najeriya da aiwatar da shirin.
Title :
Photos: Sojojin Nijeriya Sun Gina Makaranta A Sansanin Gudun Hijira A Jihar Borno
Description : Sojojin Najeriya sun burge mutane da yawa wajen gina makaranta ta yara a sansanin gudun hijira(IDP) wanda a ke garin Bama, Jihar Borno. Maka...
Rating :
5