Rahotanni da ke yaduwa a kafofin sada zumunta sunce wani faston kasar afrika ta kudu a yayin yin karama ta karya domin nuna karfin shi,ya kasha wata mata bayan ya daura babban na’uran amsa kuwa a kirjin ta. Yarinyar ta mutu sanadiyar tsinkewan hakarkari.
Mambobin cocin Mount Zion General Assembly sun ga abin mamaki a ranan lahadi yayinda wani karyan faston cocin yayinda ya daura wani babban na’uran amsa kuwa a kirjin matan ,yana mai tabbatar mata da cewan bazata ji zafi ba. Matan ta mutu bayan ta ji ciwuka a huhun ta. Fasto Lethebo Rabalango ya shirya wata Ibadan dare a cocinsa dake polokwane inda yake nuna ma mutane karfin sa kuma yace inda yesu yayi tafiya akan ruwa, zai iy komai shima.”
Ya gayyaci yarinyan gaban coci y ace mata ta kwannta . sai yayi umurni a daura mata katon amsa kuwa aka daura a cikin ta tare da cewa bazai cutar da ita ba. Bayan haka, ya hau kan cikin ta ,ya dauke mata lumfashi ,sai tayi shiru ashe ta bakunci lahira tun.
“Bayan ya zauna akan amsa kuwan da ke cikin yarinya na misalign mintina 5, sai ya tashi yace a dauke amsa kuwan daga cikin ta, amma yarinyan ta ki tashi saboda ta suma. Da kyar aka samu aka bata kulawan gaggawa sai ta tashi amma tace hakarkarinta daya ya tsinke. Daga baya da aka kaita asibiti . faston yace laifin yarinyan ne na cewan batada cikakken imani, ta kasa jure dan karamin nauyin.”
Source Naij Hausa
Title :
Photos: Fasto Ya Kashe Wata Mata Acikin cocin A Kasar Afirka Ta Kudu
Description : Rahotanni da ke yaduwa a kafofin sada zumunta sunce wani faston kasar afrika ta kudu a yayin yin karama ta karya domin nuna karfin shi,ya ka...
Rating :
5