Kungiyar Niger Delta Avengers ta ce ta tsagaita
wuta a hare-haren da ta ke kai wa kan bututayen
mai da gas a yankin Niger Delta mai arzikin man
fetur.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar
Litinin, kungiyar ta ce tana sa ran cewa
gwamnati za ta nuna da gaske take wajen
inganta yankin na Niger Delta.
Sanarwar wacce kungiyar ta wallafa a shafinta na
internet ta yi amfani da kausasan kalamai wajen
jan hankalin gwamnatin Nigeria cewa, ba za a
kawo karshen matsalar hare-hare a yankin da
karfin soja ba, don haka ta ce tattaunawa ita ce
kawai mafita.
Ita ma dai kungiyar MEND mai fafutukar 'yantar
da yankin Niger Delta ta shelanta cewa ita ma ta
shiga tattaunawa da gwamnati, ta hannun
kwamitin da Chief Edwin Clark ke jagoranta.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun
ikirarin tsagaita wuta ba da wasu da ke da'awar
yin magana da yawun kungiyar ta Niger Delta
Avengers ke yi ba , to amma wasu daga baya
suna nesanta kungiyar daga irin wannan mataki.
Bbchausa
Title :
Niger Delta Averngers ta tsagaita wuta
Description : Kungiyar Niger Delta Avengers ta ce ta tsagaita wuta a hare-haren da ta ke kai wa kan bututayen mai da gas a yankin Niger Delta mai arziki...
Rating :
5