Iyayen na Chibok da ‘Yan kungiyar BBOG sun gudanar da gangamin ne kan gazawar gwamnatin Buhari na kubutar da 'ya'yansu. Gangamin na zuwa ne bayan Kungiyar Boko Haram ta fitar da hoton bidiyon da ya nuna wasu daga cikin ‘Yan Matan Chibok da suke ci gaba da garkuwa da su.
Iyayen sun ce sun yi nadamar kuri’unsu da suka ba shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015, saboda har yanzu ya gaza ceto ‘yayansu. Kuma gwamnati ba ta yi Magana da iyalin wani daga cikin ‘Yan matan ba bayan Bidiyon da Boko Haram ta fitar.
Daga cikin ‘Yan matan da Boko Haram ta nuna a bidiyon ta bukaci iyayensu su roki gwamnati ta amince da bukatun Boko Haram domin ganin an sake su.
Kungiyar Boko Haram ta bukaci gwamnati ta saki mabobinta da ake tsare da su kafin sakin ‘Yan matan na Chibok.
Title :
Munyi Nadamar Zabe Buhari - Mutanen Chibok
Description : Iyayen na Chibok da ‘Yan kungiyar BBOG sun gudanar da gangamin ne kan gazawar gwamnatin Buhari na kubutar da 'ya'yansu. Gangamin na ...
Rating :
5