Daga Jaridar Rariya
Kwamishinan Shari'a na jihar Borno, Barista Kaka Shehu Lawan ya tabbatar da cewa tsohon Gwamnan jihar, Modu Sheriff ne ya fara tayar da rikicin Boko Haram a yankin, lamarin da ya yi sanadiyyar salwantar rayuka fiye d 20,000 ba ya ga wasu mutum sama da milyan biyu da ke gudun hijira.
Kwamishinan ya yi nuni da cewa tsohon Gwamnan na da masaniya game da yadda aka kashe Shugaban Boko Haram, Malam Mohammed Yusuf a shekarar 2009 inda ya ce shi kansa Modu ya tabbatar da cewa ya sadu da Shugaban Boko Haram din a lokacin da sojoji suka kama shi amma daga baya aka mika shi ga 'yan sanda wanda a can ne suka kashe shi.
Ya kara da cewa kafin kashe Yusuf Mohammed ya yi barazanar fallasa wadanda suke daukar nauyin tafiyarsu. Kwamishinan ya nemi a gaggauta hukunta tsohon gwamnan bisa laifin tunzura mayakan Boko Haram din.
Title :
Modu Sheriff Ne Ya Janyo Rikicin Boko Haram - Gwamnatin Bormo
Description : Daga Jaridar Rariya Kwamishinan Shari'a na jihar Borno, Barista Kaka Shehu Lawan ya tabbatar da cewa tsohon Gwamnan jihar, Modu Sheriff...
Rating :
5