GobeLimamin masallacin Annabi (S.A.W) dake birnin Madina a kasar Saudiyya, Sheikh Salah Bin Muhammad Al-Budair, zai kawo ziyarar kwanaki uku Nijeriya daga gobe Laraba.A yayin ziyarar, Sheik Al-Budair, wanda shahararren Hafizin Kur'ani ne, zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin Abuja.Haka kuma shi zai jagoranci sallolin Magariba da Isha'i a gobe Laraba da kuma sallar Asuba a ranar Alhamis.Daga bisani kuma a yammacin wannan rana ta Alhamis Shehin Malamin zai jagoranci sallolin Magrib da Isha'i a masallacin An-Nuur dake, Wuse 2 Abuja.
Title :
Limamin Masallacin Annabi (S.A.W) Zai Kawo Ziyarar Kwanaki Uku Nijeriya Daga
Description : GobeLimamin masallacin Annabi (S.A.W) dake birnin Madina a kasar Saudiyya, Sheikh Salah Bin Muhammad Al-Budair, zai kawo ziyarar kwanaki uk...
Rating :
5