Aisha Wakeel mace guda da rundunar sojin Najeriya ta ce ta na nema ruwa a jallo a kwanakin baya, ta kuma ta kai kanta, ‘yar asalin kudancin Najeriya ce daga kabilar Igbo.
A wani rahoto na jaridar Vanguard ta ce, Barisita Aisha wacce iyayenta Krista ne, ta karbi Musulunci ne a yayin da ta ke karatun shari’a a jami’ar Maiduguri. Rahoton ya kuma ci gaba da cewa, wannan bayani ya fito ne a yayin hirarta da wata jarida, a inda ta ke bayanin ayyukan da ta ke yi na samar da zaman lafiya a kasa.
A cewar ta, ta soma kokarin samar da zaman lafiya ne a cikin shekara ta 2009, tun kafin soma rikicin Boko Haram, a saboda sanayyarta da Muhammadu Yusuf da kuma alaka, ta na mai cewa, “surikinsa marigayi Alhaji Baba Fugu uba na ne na muslunci, kuma ina ziyartar gidansa... Kuma shi Muhammdu Yusuf ya so ya aure kanwata Amina, Allah ne bai yarda ba.”
Aisha wacce aka santa da sa hijab da Nigab mai rufe fuska ta kara da cewa, “Ta kai matsayin da a waccan lokaci, ina yin abinci in kuma kai wa almajiran marigayi Alhaji Fugu... Muhammadu Yusuf yana cin abincina musamman miyar agushi, mahaifinsa ya gaya masa cewa ni na ke yi.. hakan kuma ya sa sanayyata da shi ta yi karfi”.
Barista Aisha Wakeel na auren mai shari’a Wakil Gana na babbar kotun jihar Barno, kuma zamanin mulkin Jonathan ‘yan kungiyar Boko Haram sun ba da sunayensu a matsayin masu shiga tsakani a tattaunawarsu da gwamnati wanda ya faskara.
Title :
Ina Da Kyakkyawan Alaka Da ‘Yan Boko Haram –Aisha Wakeel
Description : Aisha Wakeel mace guda da rundunar sojin Najeriya ta ce ta na nema ruwa a jallo a kwanakin baya, ta kuma ta kai kanta, ‘yar asalin kudancin ...
Rating :
5