* Harin Ya Jikkata Shekau
Shugaban rundunar Sojan saman, Air Marshal Sadiqu Abubakar ya tabbatar da cewa jerin hare haren sama da jiragen yakin sama suka kai dajin Sambisa ya yi sanadiyyar hallaka mayakan Boko Haram 300.
Da yake karin haske kan batun, Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce, yayin hare-hare ta sama da aka kai ranar Juma'ar da ta gabata an kuma jikkata daya daga cikin shugabannin Boko Haram, wato Abubakar Shekau
Daga cikin manyan 'yan kungiyar ta Boko Haram da aka kashe yayin harin sun haɗa da Abubakar Mubi, da Malam Nuhu da Malam Hamman.
Sanarwar ta kuma ce, an kai harin ne a ƙauyen Taye dake yankin Gombale, dake dajin Sambisa.
Title :
Harin Jiragen Yakin Sama Ya Hallaka Mayakan Boko Haram 300
Description : * Harin Ya Jikkata Shekau Shugaban rundunar Sojan saman, Air Marshal Sadiqu Abubakar ya tabbatar da cewa jerin hare haren sama da jiragen ...
Rating :
5