Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubukar ya dora alhakin karuwar aikata miyagun laifuka a kasa a kan dabi'ar wasu gwamnonin jihohi na kin biyan ma'aikata albashi wanda a cewarsa hakan ya jefa mafi yawansu cikin yanayin yunwa.
Sarkin Muslumin ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar da ya kai wa Gwamnan Edo, Adams Oshiomole inda ya nuna damuwa bisa yanayin kunci da al'ummar Najeriya ke ciki inda ya kalubalanci shugabanni su tallafa wajen rage radadin talauci.
Ya ce "idan wata ya kare, ma'aikacin ba ya da tabbacin samun albashi da zai shiga kasuwa kuma a sanin kowa ne duk mutumin da ke cikin yunwa, to yana da hadarin gaske ga al'umma"
Title :
Gwamnoni Na Da Hannun Wajen Jefa Al'umma Cikin Yunwa - Sarkin Musulmi
Description : Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubukar ya dora alhakin karuwar aikata miyagun laifuka a kasa a kan dabi'ar wasu gwamnonin...
Rating :
5