Gwmanatin Buhari makarya ciya ce, Mu ba zamuyi sulhu da ita ba A cewar me magana da yawun kungiyar tsagerun Niger Delta wanda a ka fi sani da NDA.
Me magana da yawun kungiyar Tsagerun Agbinibo Mudoch, inda ya soki Dattijan yankin nasu da ke fafutukar ganin anyi sulhu tsakanin su da gwamnati, a cewar sa. Sam baza su sake yadda da duk wani batun tattaunawa da gwamnatin Buhari zata jagoranta ba. domin Makaryata ne a cewar sa.
Kungiyar ta kuma yi ikirarin kaddamar da hare hare ga rundunar Soji da ke aikin tsare bututun mai dake cikin ruwa, inda ya kara dacewa maya kan su sunshirya tsaf domin tunkarar rundunar ta Soji batare da Shayi ba.
Kuma ya kara da cewa har zuwa yanzu ba a kama musu ko da mutum guda daga cikin kongiyar tasu ba, inda ya fado sunayan Mutum biyu da a ka kama da cewa sam basa daga cikin su. Kungiyar tsagerun Niger Delta sun dade sun kai hare hare a kan bututan mai da ke yan kin nasu. A bangare guda kuma inda rundunar soji take kaddamar da hare hare a kan tsagerun domin kawo karshan ta addanci da yankin ke fama dashi.
Koda a jiya sai da konyir Boko haram ta sake futar da wani Bidiyo dake nuna yan matan Sakandiri da ke Chibok, inda suka nemi da gwamnati ta sakar musu mutanan su, sannan zata bada yan'matan.
Shin taura biyo zata iya taunuwa a lokaci guda, yayin da lamarin tabar-barewar tsaro ke kara ta'azzara, shun wace shawara zaku bawa gwamnati?
Title :
Gwamnatin Buhari Makaryata Ne, Baza Muyi Sulhu Ba - Niger Delta Avengers
Description : Gwmanatin Buhari makarya ciya ce, Mu ba zamuyi sulhu da ita ba A cewar me magana da yawun kungiyar tsagerun Niger Delta wanda a ka fi sani d...
Rating :
5