Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shirin sake fitar da naira bilyan 60 daga cikin kasafin kudi na bana don gudanar da wasu daga cikin manyan ayyukan a fadin kasar nan.
Kamar yadda shafin Facebook na Aso Rock Villa - Hausa ya bayyana, hakan ya fito ne daga bakin Ministar Kudi, Mrs. Kemi Adeosun.
Da wannan naira bilyan 60 da za a fitar, zuwa yanzu Gwamnatin Tarayya ta fitar da zunzurutun kudi har naira bilyan 400 daga watan Mayu zuwa yanzu.
A cewar Ministar, tuni aka biya wasu daga cikin 'yan kwangilar da za su gudanar da wasu daga cikin ayyukan, kuma da zarar sun fara gudanar da ayyukan na su hakan zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin mu musamman a cikin gida, ta hanyar shige da ficen kudade a hannun jama'a.
Minista Adeosun ta kara da cewa da zarar naira bilyan 60 din ta samu nasarar fita, za su sake zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki don sake fitar da wata naira bilyan 60 din.
Gwamnatin ta Shugaba Buhari na fitar da kudaden akai - akai domin su samu damar shiga hannun jama'a, domin samun sassauci daga sarkakiyar tattalin arzikin da kasar nan ta samu kanta a ciki.
Title :
Gwamnati Najeriya Za Ta Sake Fitar Da Bilyan 60 Na Manya Aiyuka
Description : Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shirin sake fitar da naira bilyan 60 daga cikin kasafin kudi na bana don gudanar da wasu daga cikin ma...
Rating :
5