Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da dokar da ta lamincewa gwamnatin jihar a karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ta goge duk wani wuri da aka rattaba sunan Kwankwasiya a fadin jihar.
Kudurin dokar wacce Hon Baffa Babba Dan Agundi, mai wakiltar karamar hukumar Birni ya gabatar, rahotannin sun ci gaba da cewa, an tafka muhawara a kanta a yammacin ranar, kafin ta samu amincewar mafi rinjayen yan majalisar, daga baya ta zama doka.
Bisa wannan doka, gwamnatin jihar za ta cire kalmar Kwankwasiyya a duk inda aka rubuta a wurare mallakar gwamnatin jihar, musamman gine-gine da kuma sauran wurare na jama’a, su ma rukunin gidaje na Kwanksiyya da Amana za a canza musu suna zuwa na wasu fittatun malamai a jihar.
Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa kwankwaso ne ya fito da tsarin rubuta Kwankwasiyya a duk ayyukan da gwammatinsa ta yi a jihar, a inda a waccan lokaci gwamnan ya ke cewa, ya yi hakan ne domin gudun runton aiki, hakan ta sa aka rubuta kalmar a ko’ina, kama daga jikin katangar makarantu da rufinsu, zuwa hanyoyi da gadoji, har da fiyip-fayip na ruwa da gwamnatin ta yi oda daga kasar waje.
A martanin tsohon gwamnan wanda kuma aka rika yadawa a shafukan sada zumunta da muharawa na Facebook, Rabiu Musa Kwankwaso ya na mai cewa, iya abinda za’a iya yi ke nan, amma ba‘a isa a rusa su ba, gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje, shi ne mataimakin Kwankwaso a tsawon shekaru takwas da ya yi na mulki a karo na daya da na biyu.
Title :
Gwamnati Ganduje Na Shirin Goge Duk Wani Rubutun Kwankwasiya A Jihar
Description : Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da dokar da ta lamincewa gwamnatin jihar a karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ta goge duk wani...
Rating :
5