Daga Khalid Bauchi
Da dumi-duminta daga Bauchi, a yau ne gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da bayanin korar gidan rediyon Ray Power da kuma gidan talabishin na AIT daga filin da suke watsa shirye-shiryensu.
Bayanin kokarar wanda ya baiwa gidan rediyon makonni biyu kacal da su tattara yanasu-yanasu su fice mata daga filinta, inda umurnin korar yayi nuni da cewar ba tare da bata lokaci ba, gidan rediyon ya bar wa gwamnatin jihar filinsa.
Gidan talabishin da rediyon wanda ke unguwar Turun ya samu umurnin korar ne bayan da gidan rediyon ya shahara wajen baiwa 'yan adawa damar bayyana ra'ayinsu. sanin kowane a 'yan kwanakin nan an yi ta samun tsamar siyasa a tsakanin gwamnatin jihar Bauchi da wasu, inda wasu ke amfani da gidan rediyon ray power wajen bayyana ra'ayinsu da kuma mai da martani. sanin kowa ne gidan rediyon rey fawa na kasuwa ne, iya kudinka iya shagalinka don haka suke baiwa jama'a damar bayyana ra'ayinsu zarar ka sayi time a wajensu. wannan korar dai bata rasa nasaba da wannan batun ba.
Idan baku manta ba, a shekarun baya ne dai jama'ar da suka sayi fili a nan inda gidan rediyon take gwamnati ta kwace ta ce nata ne, har wasu sun yi gine-gine da kuma daga gidajensu a yayin da hukumar land suka rushe haka aka yi ta tura rikici. na sani lokacin da ake maganar wannan filin an ce banda filin AIT amma abun mamaki yau ga shi an wayi gari gwamnati ta baiwa gidan rediyon kwanaki sha hudu ya fice mata daga fili.
To ko yaya zata kaya, ya zuwa yanzu dai jama'a sun yi zuru suna jiran matsayar gidan rediyon za su garzaya kotu ne ko zasu bai wa gwamnatin fili oho............
Title :
Gwamnati Bauchi Ta Rufe Gidan Rediyon Ray Power Da Tashan AIT
Description : Daga Khalid Bauchi Da dumi-duminta daga Bauchi, a yau ne gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da bayanin korar gidan rediyon Ray Power da kuma g...
Rating :
5