Fadar Shugaban kasa ta nesanta kanta daga matakin tuhuma tare da garkame dan kasuwan nan, Mista Joachim Iroko wanda ya saka wa karensa sunan Shugaban kasa.
Da yake mayar da martani kan zargin cewa Shugaba Buhari na da hannu wajen gurfanar da mutumin gaban kotu, Mai Magana da yawun Shugaban kasa, Garba Shehu ya nuna cewa har yanzu mutane ba su fahinci Shugaban wanda a cewarsa mutum ne mai son Zane- zanen barkwanci.
Ya kara da cewa ya kamata mutane su yi cikakken bincike game da Dalilan da ya sa 'yan sanda suka gurfanar da mutumin gaban kotu kafin su gabatar da wani zargi a kan Shugaban kasa.
Title :
Fadar Shugaban Kasa Ta Nesanta Kanta Da Garkame Mutumin Da ya Saka Wa Karensa Suna ' Buhari'
Description : Fadar Shugaban kasa ta nesanta kanta daga matakin tuhuma tare da garkame dan kasuwan nan, Mista Joachim Iroko wanda ya saka wa karensa suna...
Rating :
5