Shugaba kasa Muhammad Buhari ya fayyace cewa har yanzu mafi yawan 'yan Nijeriya ba su fahinci cewa Nijeriya ta talauce ba sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da Shugaba gidauniyar kidayar jama'a ta majalisar dinkin duniya, Farfesa Babatunde ya ziyarce shi inda ya nuna cewa gwamnatinsa na iyakacin kokarin tattalin dan abin da ya shigo hannunta ne wanda hakan ya sa mutane ba su fahinci halin da ake ciki ba.
Ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da kokari na ganin ta fadada hanyoyin samun kudade ba ya ga bangaren mai yana mai cewa Rahotanni sun nuna cewa mutane sun rungumi harkar noma wanda shi ne kadai zai kai mu ga tudun na tsira.
Title :
Dalilin Da Ya Sa Al'ummar Nijeriya Ke Cikin Yunwa - Buhari
Description : Shugaba kasa Muhammad Buhari ya fayyace cewa har yanzu mafi yawan 'yan Nijeriya ba su fahinci cewa Nijeriya ta talauce ba sakamakon fad...
Rating :
5