Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada shirin gwamnatinsa na tattaunawa da Boko Haram don kubutar da 'yanmatan Chibok.
A shekara ta 2014 ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sace 'yanmatan a wata makarantar kwana dake garin na Chibok a arewa maso gabashin kasar.
A wata hira da manema labarai a birnin Nairobi na kasar Kenya shugaba Buharin ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tattauna da jagororin kungiyar ta Boko Haram da suka san ainihin inda 'yanmatan suke.
Ya ce ya sha furta irin wadannan kalamai kan 'yanmatan na Chibok, amma yana ganin da alamu wasu na saka siyasa a batun, don haka ya fi kyau gwamnati ta tattauna kai tsaye da shugabannin kungiyar Boko Haram din na ainihi.
Ya kuma ce idan ba sa son magana da gwamnati kai tsaye, su tuntubi wata kungiya mai zaman kanta da kasashen duniya suka san da ita, ta zama mai shiga tsakaninsu da gwamnatin kan yadda za a sako 'yanmatan.
Shugaba Buharin ya yi gargadin cewa gwamnatin Najeriya ba za ta bata lokacinta kan wasu majiyoyin da ke ikirarin sun san inda 'yanmatan suke ba.
Ya ce bukatar gwamnatinsa ita ce su ga sun kubutar da 'yanmatan cikin koshin lafiya, su kuma mika su a hannun iyayensu.
Source BBC HAUSA
Title :
Buhari Zai Tattauna Da Boko Haram Akan Yan Matan Chibok
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada shirin gwamnatinsa na tattaunawa da Boko Haram don kubutar da 'yanmatan Chibok. A sh...
Rating :
5