Shugaban Muhammadu Buhari zai nemi karfin iko daga Majalissar wakilan Najeriya don aiwatar da gagarumin wani aiyuka na ceto tattalin arzikin kasar.
.
Ana saran shugaba Buhari zai mika wasikar izinin bashi dama da zarar 'yan majalissar kasar sun dawo daga hutu a watan Satumba mai zuwa don bashi damar kaddamar da wasu aiyuka na gaggawa don ceto darajar naira da samarwa matasa aiyuka tare da habaka asusun kasa na kasashen ketare da kuma farfado da masana'antun kasar da suka share shekaru da dama suna durkushe.
.
Wannan kudurin dai ya biyo bayan shawara da masana tattalin arzikin kasa suka gabatarwa shugaban kasar.
Title :
Buhari Zai Nemi Karfin Iko Na Gaggawa Daga Majalissar Kasa Don Ceto Tattalin Arziki
Description : Shugaban Muhammadu Buhari zai nemi karfin iko daga Majalissar wakilan Najeriya don aiwatar da gagarumin wani aiyuka na ceto tattalin arziki...
Rating :
5