“Na sami labarin masifar da zanga-zangar da dalibai suka yi a jihar Zamfara da abinda ta haifar, wannan jahilci ne kuma ba irin abin da zamu amince da shi bane. Ina mai tabbatar da cewa doka za ta dauki mataki akan abinda ya faru”
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne shafinsa na Twitter, imda ya yi Allah wadai da tashin hankali da kisan dalibai a makarantar kimiyya da fasaha ta Abdu Gusau Politechnic dake karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, sanadiyyar rikici akan zargin batanci da wani dalibi guda ya yi ga Annabi Muhammadu (SAW).
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin wanda ya hassada rikicin dalibi ne a makarantar, kuma ya doki wanda ake zargi da yin batancin kana ya cinnawa gidan da yake ciki wuta, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane takwas dake cikin gidan.
Title :
Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Dalibai 8 A Zamfara
Description : “Na sami labarin masifar da zanga-zangar da dalibai suka yi a jihar Zamfara da abinda ta haifar, wannan jahilci ne kuma ba irin abin da zam...
Rating :
5