Hamshakin attajirin nan, Bill Gates ya nuna damuwarsa akan sake bullar cutar shan inna a arewa maso gabashin Nijeriya, kuma kamar yadda ya taimakawa 'yan gudun hijira ya yi alkawarin taimakawa har sai an ga bayan cutar.
"Mun yi matukar farin ciki da aka ce har an kwashe shekaru biyu ba tare da samun bullar cutar ba, amma kuma bamu ji dadi ba da aka ce an samu wasu yara biyu dauke da cutar a yankin tafkin Chadi a arewa maso gabashin Njeriya.
"Yanzu mun dukufa ne wajen ganin cewa anaika da rigakafin cutar, ta yadda yara da dama za su samu, saboda ya zamanto babu wani yaro mai dauke da ita.
Ina da kwarin gwiwar cewa za mu iya, amma yanzu muna kokari muga yadda za mu tattara bayanai daga yankin kan bullar cutar saboda kada mu kuma samu aukuwar hakan a gaba.Abin farin cikin shi ne, yakin da ake yi da cutar ta Polio har yanzu ana kai.
A baya can Nijeriya ce ke da kusan rabin yawan mutane da ke dauke da cutar a duniya, har mutane suna cewa ta ina zamu fara tunkarar matsalar.
"Idan muka duba can yankin arewacin Najeirya, akwai matsaloli a fannin kiwon lafiya, amma idan muka samu muka kawar da cutar da ke bulla nan da can, to za mu shawo kan cutar baki daya".
Title :
Bill Gate Zai Bada Tallafin Rigakafin Cutar Polio A Nijeriya
Description : Hamshakin attajirin nan, Bill Gates ya nuna damuwarsa akan sake bullar cutar shan inna a arewa maso gabashin Nijeriya, kuma kamar yadda ya ...
Rating :
5