Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi bayani akan abubuwan da suka faru sukayi sanadiyar sa zama shugaban kasa a shekarar 1976 bayan kisan janar Murtala Ramat Muhammad a mumunan juyin mulki. Ya ce da farko ya ki amincewa da zama shugaban kasa saboda tashin hankalin da ya faru bayan juyin mulkin .
An kashe janar murtala ne a ranan juma’a a lokacin sallar jama’a, kiristoci ne suka kashe shi tare da mai tsaronsa a kan titi. Cif Olusegun Obasanjo wanda yake shine shugaban ma’aikatan hedkwatan koli ya ki aminfewa da hawa karagar mulku bayan rasuwan msigidansa saboda tsoron taraliyan da zai faru. Daga baya Obasanjo ya amince da daukan ragamar mulkin wanda ya mika ma gwamnatin farar hula a shekarar 1979 bayan ya kirkiro kundin tsarin mulki. Daga baya kuma ya zama shugaban kasa a shekarar 1999 karkashin jam’iyyar PDP. Ya yi shekaru 8 a fadar shugaban kasa amma daga baya bayan shekaru 8 da barin mulki , yayi hannun riga da jam’iyyar PDP kuma mara ma shugaban kasa Muhammadu Buhari dan jam’iyyar APC.
Yayinda ta ke magana tare da ma’aikatan gidan fim din a Abeokuta, Jihar Ogun a ranan litinin ,15 ga watan Augusta, Obasanjo yayi bayanin taraliyan da ya faru a kan juyin mulkin. Jaridar Daily Trust ta ruwaito Obasanjo yana mai cewa : “Kisan musulmi a ranan juma’a wanda ake zargin mabiya kirista ne suka kashe shi, ya kawo tashin hankali.”
Yayinda yake yabawa yan gidan fim din, yace fim din na tunatar da mu akan abubuwan da suka faru a baya , kana , bazasu sa mu koma rayuwar duhun da ya faru a baya ba da ta sa mu cikin halin kakanikaye. “Muna bukatan iri wannan da yawa, saboda akwai abubuwan zasu bayyana. Munada kwarewa sosai ,kuma abinda wannan fim din ke nuna.”
Babban frodusan fim din, Tonye Princewill, yace ma’aikatan na yawo fadin kasa domin neman gudun muwa da kuma tunatar da mutane tarihin kasan su. Za’a saki fim din a watan nuwamba.
Source Naij Hausa
Title :
Bayanin Obasanjo Akan Juyin Mulki murtala
Description : Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi bayani akan abubuwan da suka faru sukayi sanadiyar sa zama shugaban kasa a shekarar 1976 bayan k...
Rating :
5