Wata kotu a Afrika ta Kudu ta yanke hukuncin shekaru 10 a kurkuku ga wata mata bisa samunta da laifin sace jaririya kuma ta raine ta a matsayin 'yarta.
Matar mai shekara 50 ta musunta zargin da a ka yi mata na zamba da kuma sace jaririyar.
An dai sace jariyar, Zephany Nurse a gefen mahaifiyarta ne a wani asibiti da ke birnin Cape Town, shekaru 20 da suka wuce.
Lamarin ya fito fili ne bayan da Zephany ta yi awance da wata yarinya wadda suka yi kama sosai kuma wadda bata kaita a shekaru ba a makaranta a shekarar 2015.
Gwajin kwayoyin halittar da aka yi musu ya nuna cewa 'yan uwa ne.
Mai shari'a John Hlope ya shaida wa matar cewa ta yi wa kotu ƙarya kuma bata nuna nadama ba.
Source Arewa.qg
Title :
Barauniya Jariri Zata Sha Daurin Shekara Goma
Description : Wata kotu a Afrika ta Kudu ta yanke hukuncin shekaru 10 a kurkuku ga wata mata bisa samunta da laifin sace jaririya kuma ta raine ta a matsa...
Rating :
5