Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau wanda ake ci gaba da nema ruwa a jallo, ya fitar da wani sabon bidiyo domin jadadda shugabancinsa a haramtacciyar kungiyar.
.
Shekau ya yi wani jawabi na dakiku 24 a wani bidiyo da ya yada a Youtube,daga bisani kuma ya cire shi.
.
A wannan bidiyon wanda shugaban na Boko Haram ya hada da niyar kawo karshen cece-kucen da aka dade ana yi dangane batun ba zai kara jan ragamar kungiyar Boko Haram ba,Shekau ya ce:" Bana kaunar ganin an kashe Musulmai 'yan uwana, kuma kawo yanzu ni shugaban Boko Haram.Ban mutu ba,ban kuma jikkata ba".
.
An tabbatar da cewa an hada wannan bidiyon ne a dajin sambisa.
.
Abubakar Shekau wanda ya la'anci majalisar dinkin duniya da kuma kasashen Amurka,Faransa da Jamus na son taka muhimmiyar rawa a fagen ta'addanci na duniya.
Source Aminiya Hausa
Title :
Bana kaunar ganin an kashe Musulmai-Abubakar Shekau
Description : Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau wanda ake ci gaba da nema ruwa a jallo, ya fitar da wani sabon bidiyo domin jadadda shugabancinsa a har...
Rating :
5