Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya yi amai ya lashe bisa ikirarin da ya yi na cewa babu wata hukuma da za ta iya hukunta shi kan zargin aringizon kasafin kudi inda ya fito fili ya nuna cewa bai fi karfin doka ba.
Dogara ya nuna cewa an yi masa mummunan fahinta bisa kalaman nasa kan cewa yana da kariyar doka daga fuskantar duk wani hukunci inda ya dora laifin a kan 'yan jaridu wanda a cewarsa su ne suka yi wa kalamansa wannan makauniyar fassara.
Ya jaddada cewa zai ci gaba da yin biyayya ga bangarorin gwamnati da na shari'a kasancewa ya yi rantsuwa ya kare mutuncin tsarin mulkin Nijeriya yana mai tabbatar wa al'ummar Nijeriya ci gaba da kare martabar majalisar tarayya.
Source Rariya
Title :
Ban Fi Karfin Hukuma Ba - Yakubu Dogara
Description : Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya yi amai ya lashe bisa ikirarin da ya yi na cewa babu wata hukuma da za ta iya hukunta shi k...
Rating :
5