Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya yi ikirarin cewa ba ya da niyyar sake komawa cikin PDP kuma duk wanda ya yi kokarin jan ra'ayinsa a kan haka ba zai taba samun nasara ba.Tsohon shugaban wanda ya bayyana PDP a matsayin jam'iyyar da ke kokarin mutuwa yana mai cewa ya yanke shawarar ficewa daga PDP tun tana da sauran tasiri don haka bai ga fa'idar komawa cikinta a wannan hali da take ciki.Cif Obasonjo dai na yin raddi kan rahoton da ake yayatawa cewa an gan shi a taron kaddamar da kwamitin da zai tsara yadda PDPza ta yi zaben Shugabanninta na kasa a cibiyar Yar'adua da ke Abuja inda ya jaddada cewa hoton da ake yayatawa a lokacin yana barin cibiyar ce bayan wani taro da ya halarta.
Title :
Babu Wanda Ya Isa Ya Mayar Da Ni Cikin PDP - Obasonjo
Description : Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya yi ikirarin cewa ba ya da niyyar sake komawa cikin PDP kuma duk wanda ya yi kokarin jan ra...
Rating :
5