Tsohon ministan ilmi kuma Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya nesanta kansa daga jita-jitar dake yaduwa kan alakarsa da Kwankwaso, dakuma kungiyar Kwankwasiyya.
Tsohon Gwamnan Kano kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, ya bayyana hakan ne ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Ghali Sadiq. A wata sanarwa daya rubuta a shafinsa na kafar sadarwa ta facebook, ya bukaci magoya bayan na Sardaunan Kano da su yi watsi dawata jita-jita da ta bulla, inda har ma aka kafa wata sabuwar kungiya mai suna Shekariyya/Kwankwasiyya.
Wannan bullowar kungiyar baya rasa nasaba da dambarwar dake afkuwa, tsakanin tsohon Gwamna kuma Sanata mai wakiltar tsakiyar Kano a majalisar Dattawa, Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamna maici Abdullahi Umar Ganduje, wanda kuma tirka-tirkar ke kara daukan zafi.
Masana harkokin siyasar Kano dai tuni suka yi hassashen yiwuwar haduwar bangaren Malam Shekarau dakuma na Rabi'u Kwankwaso don yunkurin hambarar da Gwamnati maici a kakar zabe maizuwa.
Saidai har yanzu wasu magoya bayan na Malam Shekarau na cigaba da tafiya bisa tafarkin haduwa da Kwankwaso, inda tsohon Kantoman karamar hukumar Tarauni Ahmad Aruwa ke jagoranta.
Title :
Ba Wani Alakar Siyasa Tsakani Na Kwankwaso - Ibrahim Shekarau
Description : Tsohon ministan ilmi kuma Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya nesanta kansa daga jita-jitar dake yaduwa kan alakarsa da Kwankwaso, da...
Rating :
5