Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin jhar Borno ta sauke duk mambobin kwamitin ciyar da ‘yan gudu hijira abinci. Wannan saukewa ta biyo bayan zanga-zangar da ‘yan gudun hijirar suka yi ne jiya Alhamis, inda suka koka da rashin abinci da yawaitar cututtuka.
Mataimakin Gwamnan jihar Borno, Alhaji Mamman Durkwa ne ya bayyana wa manema labarai daukar wannan mataki a Maiduguri. Inda ya ce wannan bore na ‘yan gudun hijirar abin takaici ne, kuma gwamnatinsu ba za ta yarda ana kawo wa kokarinta ciyar da ‘yan gudun hijirar cikas ba, saboda kawai zari da handama irin na wasu.
mataimakin Gwamnan ya ce, gwamnatin jihar na yin kokarinta wajen ciyar da wadannan bayin Allah, amma sai ta lura cewa wasu na handame abubuwan da aka ware don ‘yan gudun hijirar.
Leadership Hausa
Title :
An Suke Kwamitin Bayar Da Abincin ‘Yan Gudun Hijira Na Maiduguri
Description : Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin jhar Borno ta sauke duk mambobin kwamitin ciyar da ‘yan gudu hijira ab...
Rating :
5